Bitar Abin Da Ya Gabata (IMANI DA ALLAH)
     face
  •   
  •  
Allah Makusanci

Icreasefontsize decreasefontsize

Bitar Abin Da Ya Gabata (IMANI DA ALLAH)

1-Bayyana alaqar da ke tsakanin imani da kwanciyar hankali da nutsuwa?

2-Mene ne imani, faxi tasirinsa a cikin al’umma?

3-Mene abin da Imani da Allah ya qunsa yake kuma yake haifarwa?

4-Wane aiki ne ya fi falala da tsada a wurin Allah Maxaukakin Sarki?

5-Faxi abin da kake ji na fa’idojin imani da Allah maxaukakin sarki a kanka, da iyalanka da al’ummarka.

6-Me Imani da Manzanni ya qunsa?

7-Mene ne ya sa son Sahabban Manzon Allah (S.A.W) yake cikin imani da shi?

8-Siffata abin da ka sani na abubuwan ban tsoron da za su faru ranar Alqiyama a jere, tun daga qananan alamomin tashin alqiyama har zuwa shigar ‘yan aljannah gidan aljannah.

9-Waxanne ne mafi mahimmancin ayyukan da suke shigar da bawa Aljannah su nesanta shi daga wuta?

10-Bayyana fa’idar imaninka da ranar alqiyama a cikin ibadarka da tsoron Allanka, da son ka ga Allah.

11-Wacce ni’ima ce ta fi girma a aljannah, kuma wace azaba ce ta fi sauqi a wuta?

   
Domin kulla alaka da mu