Ma'anar Imani Da Allah Da Haqiqarsa
     face
  •   
  •  
Allah mai aminci

Icreasefontsize decreasefontsize

Ma’anar Imani Da Allah Da Haqiqarsa

Imani na gaskiya shi ne rayuwa da farin ciki.

Ba a samun kwanciyar hankali sai dai imani da Allah mai girma da buwaya. Duk zuciyar da ba ta da imani za ta zauna cikin tsoro da ruxani da rauni da rashin kwanciyar hankali. Imanin da ake samun tsira da shi shi ne imani da Allah, wanda ma’anarsa shi ne gaskatawa da yankewa cewa Allah shi ne Ubangijin komai, mamallakinsa, mahaliccinsa, kuma Shi kaxai ya cancanta a kaxaita shi da ibada, ta sallah da azumi da addu’a da fata da tsoro da qasqantar da kai, kuma Shi ne ya siffatu da siffofin kamala gaba xaya, ya tsarkaku daga dukkan wani aibi da tawaya, mai girma da buwaya.

Imani da Allah haske ne mai kaiwa zuwa ga adalci, haske ne zuwa ga ‘yanci, haske ne zuwa ga ilimi da sani, haske ne zuwa ga shiriya, haske ne zuwa ga nutsuwa da kwanciyar hankali.

Imani da Allah ya qunshi imani da Mala’ikunsa, da littattafansa, da ranar lahira, da imani da qaddara, alkhari ko sharri. Irin wannan imanin shi ne samun arzikin mutum, kai shi ne ma Aljannar duniya ga mumini, wanda qarshensa Aljannar lahira ce Insha Allahu.

IAshar’ance: Shi ne qudurcewa da zuciya, da furtawa da harshe, da aiki da gavvai, yana qaruwa da xa’a ga Allah, yana kuma raguwa da savon Allah.

Idan an gane wannan to a sani tushen karvar ayyuka a wurin Allah shi ne Imani, saboda faxin Allah mai girma da buwaya : “Duk wanda ya yi ayyukan qwarai yana mai imani”. (Al-anbiya’a : 94)

   
Domin kulla alaka da mu