Allah Haske ne
Lallai Allah haske ne.. “Allah ne hasken sammai da qassai”
(Annur : 35)
“Haske”
Wanda ya haskaka zukatar bayinsa, waxanda suka san shi, suka yi imani da
shi, ya haskaka zukatansu da shiriyarsa.
“Haske”
Ya tafiyar da duhu da haskensa, ya haskaka sammai da qasa, ya haskaka hanyar
masu bautata masa, ya haskaka zukatansu.
Allah haske ne, hijabinsa ma haske ne, da zai yaye shi, da kyan fuskarka
ya qona iya inda ganinsa ya tsaya daga cikin halittarsa.
Lallai Allah haske ne